Sa'adu Zungur

Sa'adu Zungur (an haife shi a shekara ta 1915 - ya mutu a shekara ta 1958). Shi ne mutumin da ya fara kafa jam'iyyar siyasa a Arewacin Najeriya. Shi mawaƙi ne kuma Bahaushe. Mahaifinsa shine limamin Bauchi. Yayi makarantar firamare(elemantery school) a garin Bauchi sannan ya tafi kwaleji mai girma ta garin Katsina. Bayan ya kammala yatafi yaba technical college a jihar legas(1934). Sannan bayan yabar legas ya koyar a jihar Kano a (1940) sannan ya dawo Zaria inda yazama shugaba a makarantar magunguna a (1941), haka dai ya ƙirƙirar kungiyar hadin kan al'umma da abota a garin Zaria inda alaqarshi da marigayi Malam Aminu Kano takara bunkasa.


Developed by StudentB